5 Agusta 2020 - 12:40
China : Ziyarar Tawagar Amurka A Taiwan Barazana Ce Ga Zaman Lafiya

Sa’o’I kadan bayan da Amurka ta bayyana cewa wata tawagar jami’anta zasu ziyarci Taiwan, kasar China ta bayyana ziyarar ta Amurka da babbar barazana ga zaman lafiya.

ABNA: China dai na kallon Taiwan a matsayin wanni yankinta, tana kuma tir da duk wani yunkurin wata kasa ko gwamnati da tsibirin a hukumance.

A jiya Laraba ne gwamnatin AMurka, ta sanar cewa sakataren harkokin kiwon lafiya na kasar Alex Azar, zai kai wata ziyara a Taiwan a cikin kwanaki masu zuwa.

Idan hakan ta tabbata, ita ziyara irinta ta farko ta wani babban jami’in Amurka a cikin shekaru 41.

Marabin dai wani jami’in gwamnatin Amurka ya ziyarci Taiwan, tun a cikin shekara 1979.

342/